Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Karamin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya ce gwamnatin tarayya za ta sayar da rijiyoyin mai 17 a yayin sabunta lasisin rijiyoyin na 2024.
Sai dai Sanata Lokpobiri ya jaddada cewa 'yan kasuwa da ke da karfin jari da fasahar tafiyar da rijiyoyin ne za a sayarwa ba wai 'yan siyasa ba.
"Ban san da zamanku ba", Fubara ya yi kakkausar suka ga 'yan majalisar Rivers
Channels TV ta ruwaito karamin ministan ya bayyana hakan ne a wani taro da kungiyar fasahar man fetur ta Najeriya (PETAN) ta shirya a Texas, kasar Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Lokpobiri ya gana da kungiyar PETAN ne a yayin da ake ci gaba da taron fasahar duniya na 2024 da ke gudana a yanzu haka.
A cewarsa, matakin sayar da rijiyoyin man ga 'yan kasuwa ya kasance wani bangare na yunkurin zuba jari da bunkasa tattalin arzikin kasa.
Ministan ya bayyana cewa, a baya, ana sayar da rijiyoyin man ne ga wadanda suke nema, wanda hakan ya jawo koma baya na akalla kashi 90 na kula da rijiyoyin man.
Wannan, in ji shi, ya hana gwamnati cin gajiyar ainihin abin da rijiyoyin ya kamata su samar domin an sayar da su ne ba tare da la'akari da fasaha ko karfin kudin tafiyar da su ba.
Rahoto: Yadda likitan boge ke zubar da ciki ga ‘yan mata a Filato kan N5,000
Game da kokarin gwamnatin tarayya na canja tsarin sayar da rijiyoyin mai, jaridar The Punch ta ruwaito karamin ministan man fetur din yana cewa:
"“Mun lura da tarin rijiyoyin mai marasa aiki kuma ba wani jari da aka zuba musu a cikin shekaru ukun da suka gabata."A game da wannan, ba za mu ƙara lamuntar hakan ba, domin haka, waɗanda ke neman mallakar rijiyoyin mai dole ne su kasance masu karfin kuɗi da fasahar iya tafiyar da rijiyoyin."Wadannan rijiyoyin ba na 'yan siyasa ba ne. Muna neman 'yan kasuwa ne da ke da karfin jari da kuma fasahar gudanar da ayyukan rijiyoyin yadda ya kamata."A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito karamin ministan albarkatun man fetur na kasa, Sanata Heineken Lokpobiri ya ce gwamnati za ta kwace lasisin masu rijiyoyin mai.
Sanata Heineken Lokpobiri ya ce za a kwace lasisin gudanarwar da aka ba masu rijiyoyin man da ba basa kai wa gwamnati haraji.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbn51gZRmrpqckaOxonnGsJimppGptq9505qpmrGplnq7rYytmGarka6us8PAZqmiopmuvLq1zWakmqZdm7K1wdFmpKKmmajBorqMraCnrZKqerqtjLKgZpqRrq6vtY4%3D